Siyasar Arewa
Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya sallami shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar BSIEC daga aiki bayan amincewa da shawarin majalisar dokoki.
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta nesanta kanta da zanga-zangar yunwa da ake shirin farawa a fadin kasar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Yayin da ya rage saura awanni 48 a fara zanga zangar yunwa da tsadar rayuwa,matasa sama da miliyan guda a Arewa sun ce ba za su shiga a yi da su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasan karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano sun yi kira ga Sani Danja da ya fito takarar ciyaman din karamar hukumar.
A cikin watan Yuli, jam'iyyar NNPP ta samu koma baya a jihar Kano inda jagorori da magoya baya suka sauya sheka zuwa APC. Sanata Barau Jibrin ne ya karbe su.
'Yan majalisar jiha a Kebbi sun bayyana sauya sheka zuwa APC a daidai lokacin da ake ci gaba da kuka da yadda jam'iyyar APC ke yiwa 'yan kasar nan gashi.
Minsitan Tinubu ya ce bai kamata 'yan Najeriya su fara kuka kan halin da ake ciki a kasar nan ba, inda yace ya kamata a kara hakuri zuwa wani lokaci a gani.
An nemi asusun Rarara a kafar Facebook an rasa bayan da ya saki wata waka da ya yaba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Asabar na watan Yuli.
A makon nan ne kwatsam aka ji yadda Rarara ya saki sabuwar da ke yabawa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu duk da halin da ake ciki na yunwa da fatara a Arewa.
Siyasar Arewa
Samu kari