Siyasar Arewa
Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya yi martani kan zargin shigar da kara gaban kotu kan babban taron PDP da ak dage daga watan nan.
Tsohon Sanata, kuma toshon gwamnan Kano sau biyu, Malam Ibrahim Shekarau bayyana shirinsu na zaburar da yan kasar nan kan zaben shugabanni na gari.
Abba Kabir Yusuf ya taya Rabi'u Kwankwaso murnar ranar haihuwa. Kwankwaso ya cika shekaru 68 da haihuwa a duniya. Abba ya shafe shekaru 38 tare da Rabi'u Kwankwaso.
Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido.
Hukumar zaben jihar Kogi (KSIEC) ta sanar da zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024 inda ya ce APC ce ta yi nasara.
Yan sanda sun tarwatsa wasu matasa da ke kokarin kawo cikas a zabukan kananan hukumomi da ake cigaba da yi a ofishin hukumar zaben jihar Kaduna a yau Asabar.
An dakatar da kwamishinan ayyuka a jihar Jigawa bisa zarginsa da aikata aikin assha da matar aure a Kano. An kama shi ranar Juma'a a jihar ta Kano.
Wasu yan siyasa masu ƙarfin fada a ji a yankin Arewacin Najeriya suna kokarin neman yardar Jonathan domin tsayawa zabe a 2027 saboda dakile Bola Tinubu.
Wata gamayyar kungiyoyin APC reshen Arewa ta tsakiya, ta bayyana kudurin ta na dakatar da yunkurin tsige shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje.
Siyasar Arewa
Samu kari