Siyasar Arewa
APC ta fara zage damtse kafin zaben 2027. Jam'iyyar ta rasa Adamawa a zaben 2023. Ankafa kwamitin mutum takwas domin daidaita 'yan jam'iyyar kafin zaben.
Matasan Arewa sun ce ba dai-dai ba ne sukar Barau I Jibrin. Mataimakin shugaban majalisa ya na shan suka a kan goyon bayan kudirin harajin Bola Tinubu.
A cikin shekarar 2024, gwamnonin jihohi 12 na Arewacin Najeriya sun kashe N698.87bn kan kudaden gudanarwa, inda suka samu N205.63bn daga kudaden shiga.
Sanata Barau I Jibrin ya fuskanci bore irin na siyasa saboda kudirin haraji. An rika wa'azi a masallatan Juma'a bisa zarginsa da watsi da cigaban Arewa
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin sulhu a jihar Adamawa domin warware rikicin cikin gida da ya barke a jam'iyyar. APC ta bukaci hadin kai kafin zabe mai zuwa.
Kungiyar Arewa Consultative Forum ta janye dakatarwar da ta yiwa shugabanta, Mamman Mike Osuman bayan sukar Bola Tinubu da katobararsa kan zaben 2027.
Wasu daga cikin gwamnonin Arewa sun fara sanyi a kan kudirin haraji. Gwamna Abdullahi Sule ya ce rashin bayani ne ya haddasa adawa da kudirin daga gare su.
Matasa daga jihohin Arewa 19 sun gudanar da gangami don goyon bayan Sanata Barau Jibrin bisa rawar da yake takawa kan dokokin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar.
Sanatocin Arewa sun gudanar da taron sirri bayan kudurin sake fasalin haraji ya tsallake karatu na biyu, inda aka tura shi zuwa Kwamitin Kudi na majalisar dattawa.
Siyasar Arewa
Samu kari