Siyasar Arewa
Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi ya goyi bayan soke rajistar babbar jam'iyyar adawa ta ADC da wasu jam'iyyu hudu.
Dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya samu tikitin takarar majalisar wakilai domin wakiltar mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua a 2027.
Gwamna Mai Mala Buni da 'yan APC a jihar Yobe sun amince da tsohon sakataren gwamnati jihar Baba Malam Wali ya yi takarar gwamna a zaben 2027 mai zuwa.
A labarin nan, za a ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karyata rade-radin cewa gwamnatinsa ta ki cika alkawari ga yankin Arewa maso Gabas.
Tsohon IGP Mohammed Adamu ya yi watsi da tsarin maslahar da ake ƙoƙarin yi wa Sanata Ahmed Wadada a Nasarawa, inda ya sayi fom ɗin takara don fafatawa a APC.
A labarin nan, za a ji Abdullahi Sa'idu, shugaban ƙaramar hukumar Kiru da ke jihar Kano ya ba wa matan da ke hannunsa akalla 500 tallafin abin wanki da wanke-wanke.
Gwamna Babagana Zulum ya goya wa Mustapha Gubio baya domin gadon kujerarsa a 2027, matakin da ake ganin zai zama barazana ga haɗin kan APC a jihar Borno.
Mata da matasan ƙaramar hukumar Toro sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan jagorancin Sanata Shehu Buba, suna zarginsa da gazawa.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya zaɓi Sanata Ahmed Aliyu Wadada ne bayan tuntuba, yana mai cewa burinsa shi ne samun ɗan takarar da zai fi sauƙin cin zaɓe.
Siyasar Arewa
Samu kari