Siyasar Arewa
Primate Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan dogaro da gwamnonin Arewa wajen zaɓen 2027, yana cewa wasu na iya juya masa baya a ƙarshe.
A shekarar 1991, Mariya Abdullahi ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin yar majalisar wakilai a mazabar Bakori da Danja da ke jihar Katsina.
Jam’iyyar ADC ta ayyana Kassim Gana Geidam a matsayin ɗan takarar gwamna a Yobe yayin da APC ta marawa Baba Wali baya, lamarin da ya kawo cikas ga Ahmad Lawan.
Tsohon gwamna, Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a karkashin ADC domin bai wa tsohon kwamishinan kudi, Faruk Malami-Yabo.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun mayar da fom din neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC a zaben 2027 da ke tafe.
Gwanma Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa ba zai nemi takarar Sanata ba a zaben 2027 mai zuwa. Ya bayyana cewa an matsa masa lamba amma ya ki amincewa.
Jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani a jihohin Gombe, Nasarawa, Yobe da Taraba da Oyo saboda gaza cimma yarjejeniya ta hanyar sulhu.
Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya sanar da cewa jam'iyyar ADC bata ba shi takara ba. Hakan ya nuna cewa ba zai yi wa jam'iyyar takarar gwamna ba.
Mai neman takarar gwamna a Taraba a karkashin jam'iyyar APC, David Sabo Kente ya ce dole a yi adalci ko jam'iyyar ta rushe a zaben 2027 da ke tafe.
Siyasar Arewa
Samu kari