Siyasar Arewa
Matasan kungiyar APC Youth Alliance sun yi martani ga Sanata Kabiru Marafa bayan kirkiro tsagin jam'iyyar APC a jihar Zamfara. Sun ce ba zai yi tasiri ba.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya zargi wasu yan siyasa a Arewa da kokarin juya baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad III, sarkin Musulmi da ke Sokoto, ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin bin duk wata doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya.
Ana fargabar sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai a cikin jam'iyyar APC bayan da Sanata Kabiru Marafa ya farfado da tsagin jam'iyyar da ya ke jagoranta a Zamfara.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya karbi bakuncin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, a wata ziyarar ban girma a gidansa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kare sukar da wasu ke yi ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cewa ya tsani 'yan Arewa, ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma ta amince da wani tsarin magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta a halin yanzu. Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan.