Bikin Sallah
Gwamnatin tarayya karƙashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta ayyana Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun karamar sallah, ta taya musulmai murna.
A ranar Asabar mai zuwa, 29 ga watan Ramadan daidai da 29 ga watan Maris, za a fara dubam jinjirin watan karamar Sallah a Najeriya, Saudiyya da ƙasahen da dama.
Masanin taurari a Najeriya Simwal Usman Jibrin ya bayyana cewa ranar Asabar za a haifi jinjirin watan Shawwal. Ya ce sai dai ba lallai aga watan a ko ina ba.
Wasu daga cikin mazauna Kano sun bayyana fatan sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki za su ajiye batun gudanar da hawan Sallah don kare rayukan jama'a.
Malamin addinin musulnci, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu Triumph ya roki sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero a kan ya hakura da batun hawan Sallah a jihar.
Rundunar ƴan sandan Kano ta yi magana kan yadda ake shirin gudanar da hawan Sallah karama a jihar, inda ta ce ta samu labarin sarakuna biyu na shirin hawa.
Dan Majalisa mai wakiltar Bakori da Ɗanja a Majalisar Dokoki ta Ƙasa ya raba tallafi da goron Sallha ga al'ummar mazaɓarsa, an raɓa kimanin N110m.
Wasu miyagu sun farmaki masallaci a jihar Kaduna yayin da masallata suke tsaka da gudanar da ibada. 'Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da kai harin.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nada sababbin mukamai, inda aka zabo da yawa daga cikinsu matasan 'yan siyasa, daga ciki har da Auwal Lawan Aramposu.
Bikin Sallah
Samu kari