Sabon Farashin Man Fetur
Matasa da masu keke NAPEP sun yi zanga zangar adawa da karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi. Sun bukaci a rage kudin mai domin saukaka rayuwa.
Kungiyar kwadago ta yi umarnin gaggawa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dawo da kudin mai da ya kara. NLC ta ce za ta zauna domin daukar mataki.
Malamin addinin kirista, kuma jagora a cocin Methodist da ke Abuja, Rabaran Dr. Michael Akinwale ya ce bai dace yan kasar nan su rika kushe gwamnatin Tinubu ba.
Kungiyar MAN ta ce da yiwuwar farashin kayayyaki ya kara hauhawa sakamakon ƙaruwar kuɗin litar man fetur a Najeriya, ta ce kananan sana'o'o zasu shiga matsala.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana kan fita zanga zanga bayan gwamnatin Bola Tinubu ta kara kudin man fetur a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa druruwan 'yan adaidaita sahu sun mamaye titunan Kano domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karin farashin man fetur.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi martani kan karin kudin man fetir da aka yi a kasar nan. Kungiyar ta ce shugaban kasa Bola Tinubu ya yaudare ta.
Farashin man fetur ya ƙara yin tashin gwauron zabi a Kano yayin da Lita ta tabo N1,200 a gidajen man ƴan kasuwa a Kano, a NNPC kuma farashin lita N904.
Matatar man Dangote za ta rika samar da jimillar lita miliyan 25 na man fetur ga kasuwannin Najeriya a kullum daga watan Satumba. Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari