Sabon Farashin Man Fetur
Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon abinci ba zai magance komai ba.
Kamfanin man NNPC ya bayyana cewa tsadar da fetur din Dangote ya yi ya sa 'yan kasuwa a Najeriya ba za su iya sayen man kai tsaye daga matatar ba.
Bankin CBN ya ce cire tallafin man fetur da matsalolin tsaro za su iya zama barazana ga tattalin arzikin Najeriya. CBN ya ce asusun wajen Najeriya zai iya ci baya.
Femi Falana ya ce kamfanin mai na kasa NNPC ya karya dokar PIA da ta bai wa kasuwa damar ƙayyade farashin man fetur a Najeriya, ya ce babu ruwan gwamnati.
A wannan labarin, za ku ji cewa wasu yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa dole su rika nema tare da shigo da kamfanin man fetur daga kasashen waje.
Matatar Dangote da kamfanin man Najeriya na NNPCL sun yi sabani kan yadda farashin mai yake a tsakaninsu. Dangote ya ce ba a Naira ya sayar da mai ba ga NNPCL.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana farashin da zai sayar da fetur wanda ya samu daga matatar Dangote da ke a jihar Legas. Farashin na watan Satumba ne.
Kamfanin mai NNPCL ya fara lodin man fetur daga matatar Dangote a ibeju Lekki Axis na Legas. An rahoto cewa motocin NNPCL sun fara dakon man a ranar Lahadi.
Bayanan da aka samu na nuni da cewa farashin fetur na iya saukowa zuwa N857 da N865 kan kowace lita. Wannan na zuwa ne yayin da NNPCL ya fara jigilar man Dangote.,
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari