Jihar Rivers
Gwamnonin Kudu maso Kudu da wasu 'yan siyasa sun fara maganar sasanta rikicin jihar Ribas. Nyesom Wike ya ce ba shi da adawa da sulhu da gwamna Simi Fubara.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a a Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana cewa dole ce ta tilasta wa Bola Ahmed Tinubu kakaba dokar ta baci a Ribas.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana takaicin yadda majalisa ta saba kundin tsarin mulki wajen tabbatar da dokar ta ɓaci da Bola Tinubu ya sa a Ribas.
Tsohon ministan Jonathan ya ce rashin iya tafiyar da mulki ne ya haddasa rikicin Osun, yana mai bukatar a dauki matakin dokar ta baci domin kare rayuka da dukiyoyi.
Fashewa ta sake aukuwa a Soku, jihar Rivers, lamarin da ya kara jefa damuwa kan tsaron wuraren hakar mai, yayin da ake kira da a gudanar da bincike.
Kwanaki bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi, ya bayyana a bainar jama'a karo na farko bayan dakatar da shi daga ofis.
Kungiyar SERAP ta dauki matakin shari'a kan dakatarwar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokokin Rivers.
Karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya taso Rabiu Musa Kwankwaso a gaba kan kalaman da ya yi dangane da dokar ta baci a Rivers.
Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka ya caccaki mulkin dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce Tinubu ya yi haka ne domin dawo da soka.
Jihar Rivers
Samu kari