Jihar Rivers
Kungiyar IYC ta duniya ta kalubalanci shugaban riko na jihar Ribas bayan ya sanar da dakatar da jami'an gwamnati da gwamna Siminalayi Fubara ya nada.
Wasu daliban lafiya sun nuna kin amincewa da karbar matar shugaban kasa, Remi Tinubu a matsayin uwarsu a yankin Neja Delta bayan dakatar da Fubara.
Shugaban riko na jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas ya sauke dukkan masu mukaman da gwamna Siminalayi Fubara ya nada. Ibok-Ete Ibas ya sanar da haka ne a ranar Laraba.
A kokarinta na yaki da cin hanci, Majalisar wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman cire kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni.
Gwamnonin jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, da Zamfara sun maka Tinubu a Kotun Koli kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Kungiyoyin kwadago a Ribas sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, inda suka bukaci Shugaba Tinubu da ya janye dokar ta-baci da ta hana a biya albashin ma’aikata.
Kotun koli ta bayyana dalilin ganin alkalin da ya yi hukunci a jihar Rivers zaune da Nyesom Wike. Kotun koli ta ce alkalin ya je taron ne saboda karrama shi.
Babbar kotun Abuja na shari'a kan nadin Ibas a Rivers. Lauya ya bukaci kotu ta hana shugaban ƙasa tsige gwamna ko nada shugaban riko a kowace jiha.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin ayyana dokar ta baci a juhar Rivers tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da 'yan majalisa.
Jihar Rivers
Samu kari