Jam'iyyar PDP
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya nada Sani Ahmadu Ribadu, wanda ya kasance kani ne ga Malam Nuhu Ribadu, matsayin sabon Sarkin Fufore.
Mr. Nyesom Wike ya ce jihar Ribas ba ta taba samun gwamna adali kuma mai nagarta kamarsa ba, ya ce Odili ne ke zuga Fubara ya take umarnin shugaban kasa.
Yayin da rikicin gwamnatin Edo da shugabannin ƙananan hukumomi ke ƙara tsananta, ciyamomi 2 da ƴan majalisarsu watau Kansiloli 13 sun fice daga PDP zuwa APC.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai tafi ziyarar kwana ɗaya a jihar Enugu gobe Asabar, zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Gwamna Mbah ya gama.
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ba zai ci gaba da jure wulakancin da ake masa daga ɓangaren Nyesom Wike ba inda ya ce ya gama hakuri kan haka.
Dattawan jihar Rivers sun ja kunnen Wike inda suka ce ya tabo stuliyar dodo tun da ya tabo tsohon gwamnan jihar Peter Odili. Sun bukaci Wike ya ba Odili hakuri.
An samu tsautsayi inda mutane da dama suka samu raunuka kan rigimar shugabancin kananan hukumomi a jihar Edo, inda aka tsige shugabanni guda biyu.
Dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya musanta rade-radin tattaunawar hadaka da PDP, NNPP ko wata jam’iyyar siyasa inda ya ce ba gaskiya ba ne.
Tsohon shugan APC, Salihu Lukman ya ce sun fara haduwa domin kayar da Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa. Salihu Lukman ya ce suna hada kai da 'yan APC.
Jam'iyyar PDP
Samu kari