Jam'iyyar PDP
Abokin takarar Atiku Abubakar a 2023, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa sun koma APC ne saboda kawo cigaba a jihar Delta. Ya ce dole ne a rika samun canji a siyasa.
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya gargadi kan ƙoƙarin raunana PDP, yana mai cewa lalata jam'iyyar na iya haifar da rushewar dimokaradiyya a Najeriya.
Tsohon Gwamnan Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya caccaki ’yan siyasa kan yadda suke sauya sheka ba tare da adawa ta hakika don talakan Najeriya.
Kenneth Okonkwo ya ce dole ne jam’iyyun adawa su kafa kawance domin kayar da Tinubu a 2027. Ya ƙara da cewa, APC za ta fuskanci kalubale nan ba da jimawa ba.
Gwamna Nasiru Idris ya musanta jita-jitar sauya sheƙa daga APC zuwa hadar Atiku, yana mai cewa zai kasance mutum na ƙarshe da zai bar jam'iyyar APC.
PDP na shirin taron gaggawa bayan sauya sheƙar 'ya'yanta akalla 300 zuwa jam'iyyar APC saboda rikice-rikicen cikin gida a matakin jihohi da ƙasa.
Dr. Jibril Mustapha ya bukaci Jonathan da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027, yana mai cewa Najeriya na bukatar shugaba mai kishin kasa da hadin kai.
Chief Olabode George ya tabbatar da cewa Najeriya ba za ta zama ƙasa mai tsarin jam’iyya ɗaya ba, yana mai fatan PDP za ta farfaɗo bayan taron NEC.
Bayan komawa APC a Najeriya, Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi alkawarin kawowa Bola Tinubu kuri'u miliyan 1.4 a zaben shekarar 2027.
Jam'iyyar PDP
Samu kari