Jam'iyyar PDP
Davido ya yi wasu baituka a sabuwar waƙarsa da ke nuna Gwsmna Ademola Adeleke na shirin tattara kayansa ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Hadimin ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan ficewa daga jam'iyyar PDP.
Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dalilin da ya ssnya ya yi aiki don tabbatar da cewa Atiku Abubakar da PDP sun fadi zaben 2023.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya yi martani kan kalaman da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi a kan tsohon mataimakin shugaban ƙasan.
Sauya shekar Atiku daga jam'iyyar PDP ta jawo hankalin manyan ƴan siyasa a jihar Adamawa, manyan jiga jigai sun fara tururuwar komwa jam'iyyar haɗaka ADC.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Dele Momodu ya sauya sheka zuwa ADC a jihar Edo. Momodu ya ce 'yan ba ni na iya sun mamaye jam'iyyar PDP.
Daya daga cikin hadiman Atiku Abubakar ya bayyana cewa an tono wasikar murabus dinsa daga jam’iyyar PDP mai adawa ba tare da izini ba a bainar jama’a.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana ɓacin ransa kan yadda Atiku ya fitar da wasiƙar barin PDP ana tsakiyar jimamin rasuwar Muhammadu Buhari.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ko kaɗan tafiyar Atiku Abubakar ba zai wa PDP illa ba, yana mai cewa jam'iyyar tana nan da ƙarfi da farin jininta.
Jam'iyyar PDP
Samu kari