Jam'iyyar PDP
Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta umarci jam'iyyar PDP ta dakatar da shirinta na yin babban taronta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a watan Gobe.
Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta tunbuke dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Gummi/Bukkuyum, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda ya koma APC.
Sababbin bayanai sun nuna Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba na dab da barin PDP zuwa APC bayan tattaunawa ta sirri da manyan yan APC a birnin Abuja.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya cika baki kan zaben shekarar 2026. Ya bayyana cewa babu wani dan siyasan da zai iya kayar da shi a zaben gwamna.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Jam'iyyar PDP ta rasa dukkanin 'yan majalisar wakilan da take da su a jihar Enugu. Dukkan 'yan majalisun sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC mai mulki.
Jam'iyyun adawa na LP da PDP sun sake samun koma baya a majalisar wakilan Najeriya. Wasu daga cikin 'yan majalisar da suke da su sun koma APC mai mulki.
Sanatan Bayelsa ta Gabas, Benson Agadaga ya sanar da sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance a zaman Majalisar Dattawa na yau Laraba.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Zamfara ta rasa daya daga cikin 'yan majalisun da take da su. Dan majalisar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai adawa.
Jam'iyyar PDP
Samu kari