Jihar Plateau
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da hotun da ake yaɗawa ana cewa wai ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, ya faɗi masu hannu.
Wani dan Majalisar Tarayya daga jihar Plateau, Ajang Iliya ya koma jam'iyyar APC a yau Alhamis 12 ga watan Disambar 2024 wanda hakan ya jawo tarzoma a majalisar.
Sojojin Najeriya sun cafke rikakken dan bindiga mai garkuwa da mutane da yake raba makamai a jihohin Filato, Kaduna da Zamfara a yankin Bassa na Filato.
Dan majalisar wakilai ya yi mamakin yada labarin mutuwarsa. Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya ce ya na ta shan kiraye-kirayen waya.Ya ba wa masu yada labarin karya shawara.
Rahoto ya nuna cewa majalisar tarayya ta amince da kudurin da aka gabatar gabanta na kafa jami'ar ma'adanai ta tarayya a garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi wa Janar Yakubu Gowon martani. Obasanjo ya ce bai taba sanin cewa Gowon ya nemi ka da a kashi ba.
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya bayyana jin dadinsa da ganin Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya a 1999 bayan ya fito daga gidan yari.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe wani dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa. Dattijon na da matsayin sarauta a Bokkos a jihar Filato.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun taru a jihar Plateau domin nemo hanyoyin kawo hadin kai da zaman lafiya a jam'iyyar tare da dawo da martabarta a idon yan Najeriya.
Jihar Plateau
Samu kari