Jihar Plateau
Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya fito zanga-zangar da aka fara yi a fadin kasar nan kan tsadar rayuwa da wahalar da ake sha a kasa.
Wani malamin addini a jihar Filato ya jagoranci matasa zuwa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Filato. Dakta Isa El-Buba ya ce wahalar rayuwa ta yi yawa.
Gwamnatin jihar Plateau ta fito ta yi martani kan zargin cewa ta ware N3.9bn domin siyo motocin alfarma ga gwamnan jihar. Ta fadi yadda abin yake.
Yusuf Adamu Gadgi na wakiltar mazabar Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai a karkashin inuwar jam'iyyar APC. Ya taba rike mukamin mataimakin kakakin majalisa.
Masu ruwa da tsakin APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara tuntuɓa da neman Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya tattaro kayansa ya baro jam'iyyar PDP.
'Yan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau mai suna Yakubu Muhammad a daren jiya Alhamis 18 ga watan Yulin 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an tsinci gawar wani sojan Najeriya da ya yi ritaya a cikin daki a birnin Jos na jihar Plateau. Za a fara bincike kan lamarin.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cafke miyagu takwas da ake zargi aikata manyan laifuffuka a jihar Filato dauke da tarin makamai, ana neman wasu ruwa a jallo.
Gwamnatin jihar Filato ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin karrama wadanda suka mutu a sakamakon ginin makaranta da ya rufta a garin Jos.
Jihar Plateau
Samu kari