Daga Shan Wani Magani, An Garzaya da Dalibai Fiye da 60 Asibiti a Jihar Katsina
- Dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, jihar Katsina, sun kwanta a asibiti bayan sun nuna alamun rashin lafiya
- Rahotanni sun nuna cewa an garzaya da daliban zuwa asibiti cikin gaggawa jim kaɗan bayan ssun sha wani magani
- Kwamishinan ilimi na jihar, Yusuf Sulaiman Jibia, ya ce dukkan daliban sun warke kuma ana shirin mayar da su makaranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewaan garzaya da dalibai 64 na makarantar kimitta ta gwamnati da ke Batagarawa a jihar Katsina, zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
An kwantar da daliban a asibiti ne bayan sun kamu da rashin lafiya, har wasu sun fita daga hayyacinsu sakamakon shan wani maganin rigakafi.

Source: Twitter
Gwamnatin Katsina ta kwantar da hankali
Leadership ta ruwaito cewa lwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Katsina, Yusuf Sulaiman Jibia, ya bukaci a kwantar da hankula kan wannan lamari da ya faru
An garzaya da daliban zuwa babban Asibitin Ahmadu Rimi da Asibitin Mata da Yara na Turai Yar’Adua da ke Katsina, bayan sun fara amai, jin ciwon ciki da kuma jiri jim kaɗan bayan shan maganin.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin daliban sun isa asibitocin a sume, lamarin da ya jefa iyaye da al’ummar makarantar cikin fargaba.
Wane hali daliban suke ciki?
Yusuf Jibia ya tabbatar da cewa dukkan daliban 64 sun warke bayan samun kulawar likitoci, kuma ana shirye-shiryen mayar da su makaranta.
“Daliban da abin ya shafa sun warke sarai, kuma muna shirye-shiryen mayar da su makaranta,” in ji kwamishinan.
Ya bayyana cewa hukumomin kula da lafiya s matakin farko ne suka gudanar da aikin bayar da maganin tare da haɗin gwiwar ƙaramar hukumar Batagarawa, a wani shiri na rigakafi da shawo kan cutar Bilharzia a tsakanin yaran makarantu.
Kwamishinan ya tabbatar wa iyaye cewa gwamnati za ta gudanar da bincike domin gano abin da ya faru. Ya ƙara da cewa ana ba daliban abinci kafin a mayar da su makaranta.
Abin da likitoci suka bayyana
Tun da farko, Daraktan lafiya na Asibitin Ahmadu Rimi, Dakta Auwal Sani, ya tabbatar da cewa an kawo wasu daga cikin daliban asibitin a sume, amma daga baya suka fara samun sauƙi bayan jinya.

Source: Original
Wasu dalibai biyu da abin ya shafa, Abubakar Muhammad Khairi da Hassan Muhammad, sun ce jami’an lafiya sun auna tsayinsu kafin su ba su maganin.
A cewarsu, yawan maganin da aka ba daliban ya bambanta. Wasu sun samu uku, wasu biyu, yayin da aka ba wasu guda ɗaya.
Sai dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da ainihin musabbabin matsalar da daliban suka fuskanta ba.
Cutar kwalara ta barke a Gombe
Kun ji cewa Gwamnatin Jihar Gombe ta ayyana barkewar cutar kwalara a ƙauyen Kedo, da ke gundumar Todi a ƙaramar hukumar Billiri.
Gwamnatin ta ayyana barkewar cutar ne bayan rahotannin gudawa da amai da suka yi sanadin mutuwar mutane biyu a farkon watan Oktoban 2026.
Asali: Legit.ng

