Rikicin PDP
Kusa a jam'iyyar PDP, Cif Bode George ya gargadi Atiku Abubakar da Nyesom Wike da su cire son zuciyar da ga haddasa rikicin da PDP ke fama da shi na tsawon lokaci.
Yayin da rikicin PDP ya ki ci ya ki cinyewa, Sanata Ned Nwoko ya fice daga jam’iyyar kuma ya koma APC, yana mai bayyana rikice-rikicen jam’iyyar a matsayin dalilai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin jam'iyyar guda 12 suna wata ganawa a asirce a Asaba, babban birnin Jihar Delta, ba tare da bayyana dalilin ba.
An yi mamaki da Atiku Abubakar bai halarci taron PDP na Arewa maso Gabas ba. PDP na shirin kawo gyara a shugabancinta don tabbatar da sulhu da karfafa jam’iyya.
Tsohon ɗan majalissr tarayya, Hon Tajudeen Yusuf ya ce girman kan Atiku da kuma shiga hurumin Allah inda ya ɗauka dole shi zai ci zaɓe ne ya jawowa PDP faɗuwa.
Gwamnonin PDP karkashin Sanata Bala Muhammad sun kira taron gaggaya a jihar Delta kan rikicin PDP. Za a yi taron ne bayan an ba hamata iska a taron PDP.
Shugaban majalissr amintattun PDP watau BoT, Sanata Adolphus Wabara ya jaddada buƙatar shirya taron NEC kamar yadda aka tsara domin warware rigingimu.
Dakarun sojoji, ƴan sanda da wasu jami'an tsaro sun kai ɗauki babbar hedkwatar PDP ta kasa da ke Abuja bayan rigima ta ɓarke a taron Majalissr amintattau BoT.
Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun yi 'yar arangama kan kujerar sakataren PDP na ƙasa a wurin taron ƴan majalisar amintattu watau BoT.
Rikicin PDP
Samu kari