Rikicin PDP
Ana zargin 'yan bangar siyasa da jam'iyyar PDP ta yi hayarsu, sun kashe shugaban karamar hukumar Irewole, jihar Osun lokacin da fada ya barke kan hukuncin kotu.
'Yan majalisar dokokin Kaduna sun sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda nasarorin Gwamna Uba Sani, suna mai alkawarin ci gaba da kawo zaman lafiya da ci gaba a jihar.
Jam’iyyar PDP a Kudu maso Kudu ta shiga rikici kan taro a Benin. Cif Omemu ya kira shugabanni su kauracewa taron, yana zargin an kulla wata makarkashiya.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Adolphus Wabara. Jam'iyyar ta fadi laifukan da ake zarginsa da su.
Hon. Amos Magaji ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC saboda rikicin cikin gida, inda Chinda ya bukaci a ayyana kujerarsa a matsayin babu kowa.
Sakataren PDP da ake ta tababa kan kujerarsa, Sanata Sam Anyanwu ya zargi gwamnonin PDP da kokarin tsige shi saboda dangantakarsa da Nyesom Wike.
Sanata Barau Jibrin da Bamidele sun maida martani ga Abba Moro yayin da ya yi ikirarin cewa sauya sheƙar Sanata Ned Nwoko ta saɓa wa doka saboda PDP ba rabe ba.
Sanatan Ned Nwoko, mai wakiltar mazaɓar jihar Delta ta Arewa ya canza sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance a zauren Majalisar Dattawan Najeriya.
Majalisar amintattun PDP ta ƙasa watau BoT ta kira taron gaggawa a babban birnin tarayya Abuja domin tattauna halin da jam'iyyar ta tsinci kanta a ciki.
Rikicin PDP
Samu kari