Rikicin PDP
Tsohon mai magana da yawun PDP, Kola Ologbondiyan ya yi ikirarin cewa gwamnoni da sauran ƴan siyasar da ke komawa APC mafutarsu kawai suke dubawa.
Wike ya nemi PDP ta kai tikitin 2027 Kudu. Ya ce ware tikitin 2023 zuwa Arewa ya haifar da rikici amma ana ganin Wike na kokarin hana Atiku takara a jam'iyyar ne.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa son rai ka iya karisa murkushe PDP tun kafin zaɓen 2027, yana mai cewa jam'iyyar ba za ta kai labari ba.
Saraki zai jagoranci kwamitin dinke barakar PDP. An ce kwamitin zai tabbatar da cewa an yi taron NEC da babban taron jam'iyyar cikin nasara don tunkarar 2027.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa kamar APC da PDP ba su da bambanci domin duk manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.
Jam'iyyar APC ta sake wargaza shirin jam'iyyun adawa inda tsohon gwamnan Delta, Dr. Emmanuel Uduaghan da ƴarsa wacce kwamishina ce suka warsar da PDP.
Kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Rt. Hon Emomotimi Guwor ya sanar da sauya shekarsa tare da ƴan Majalisa 21 daga PDP zuwa jam'iyyar APC s hukumance.
Gwamnonin PDP sun samu komawa a ƙarar da suka kalubalanci matakin Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas, gwamnan Delta ya janye daga ƙarara bayan =a koma APC.
Tsohon shugaban PDP na Anambra, Cif Ndubuisi Nwobu, ya caccaki Nyesom Wike kan kasancewa a jam’iyyar APC tare da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.
Rikicin PDP
Samu kari