Jihar Oyo
Kungiyar Musulmin Oyo ta bukaci Seyi Makinde ya nuna adalci da daidaito ta hanyar mara wa dan takarar Musulmi baya a zaben gwamnan jam'iyar PDP mai zuwa.
Gwamnatin Oyo ta gargadi mazauna jihar da masu sayar da dabbobi kan sayar da shanu da raguna a manyan tituna yayin bikin babbar salla mai zuwa a kananan hukumomi 33.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya nuna kwarin gwiwar cewa jam'iyyarsa ta PDP za ta samar da shugaban kasa a 2027. Makinde ya bukaci hadin kai a jam'iyyar.
Tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ba shi izinin barin mukaminsa domin fara shirye-shiryen neman kujerar gwamnan Oyo.
Hausawa da ke jihar Oyo sun barke da zanga-zanga bayan wani dan sanda ya kashe wani dan jihar Zamfara da ya ke tuka babur a jihar Oyo. Yan sanda sun yi magana.
Shugabannin jam'iyyar APC a jihar Oyo sun goyi bayan Sanata Sharafadeen Alli ya yi takarar gwamna a 2027 maimakon ministan makashi da ya yi murabus, Bayo Adelabu
A labarin nan, za a ji wasu manyan APC a jihar Oyo, Akeem Adetoyese da Mogaji Abiola Oyeyemi sun yi zargin cewa an nada mutumin da ba ɗan jam'iyya ba minista.
Bidiyon tsiraicin fitacciyar mai sayar da maganin gargajiya a Najeriya, Sisi Alagbo ya bazu a kafafen sada zumunta. Ta nemi afuwar jama'a kan bidiyon.
Shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC a Kudu maso Yamma, jihohin Yarabawa 6 na Najeriya ta shirya kifar da shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.
Jihar Oyo
Samu kari