Jihar Oyo
20 ga Agusta ta kowace shekara na zama ranar hutu a jihohin Oyo, Lagos, Ogun da Osun don bikin Isese, amma Ondo da Ekiti ba su amince da ranar hutun ba tukuna.
Kungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta ce harin dodon gargajiya kan limami ya saba wa doka ne kuma gwamnati ta binciki Lobanika da dukan masu hannu.
A watan Yulin 2025, sarakuna uku daga jihohi daban daban a Najeriya sun riga mu gidan gaskiya, ɗaya daga ciki shi ne Sarkin Gusau, Ibrahim Bello.
PDP za ta gudanar da babban taronta a Ibadan daga 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. Ta dauki matakin doka kan mambobin da suka sauya sheka bayan lashe zaɓe.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Oyo, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin ya yi alhinin rasuwar babban limamin Oruwa, Sheikh AbdulKareem Olore, ya roki Allah Ya gafarta masa.
Tanka dauke da lita 33,000 na man fetur ta fashe a Celica, Ibadan, kusa da gidan man NNPCL bayan ta yi karo da mota sakamakon shanyewar birki, gobara ta tashi.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ko kaɗan tafiyar Atiku Abubakar ba zai wa PDP illa ba, yana mai cewa jam'iyyar tana nan da ƙarfi da farin jininta.
Jihar Oyo za ta kashe N7.7bn don siyan jiragen yaki guda biyu da za su taimaka wa Amotekun da jami'an tsaro wajen yaki da masu garkuwa da mutane.
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya bayan mulkinsa na shekara guda, ya bar gadon zaman lafiya da ci gaba a Ibadan.
Jihar Oyo
Samu kari