Jihar Osun
Gwamna Ademola Adeleke dan kasuwa ne kafin ya tsunduma harkar siyasa, ya je majalisar dattawa gabanin ya samu nasarar zama gwamnan jihar Osun a zaben 2022.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi kira ga abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji da ya zo su hada hannu don ci gaban jihar..
A labarin nan, za a ji cewa dan takarar gwamnan jihar Kano, Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzi ya bayyana irin nasarar da za a samu a kan gwamnatin Abba.
Ƴan siyasan da zuri'ar Adeleke ta haifar a tarihin Najeriya shi ne abin da rahoton nan ya kawo. Kafin yanzu, mahaifin gwamna mai-ci da yayansa duk sun yi siyasa.
Jam'iyyar APC ta Osun na nazarin sakamakon zaɓen gwamna na 2026, yayin da jam’iyyar ke tunanin kai ƙara kotun zaɓe domin ƙalubalantar sakamakon zaben.
Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord ya lashe zaben wa’adin biyu a jihar Osun da kuri’u 511,067, yayin da Bola Oyebamiji da APC suka sha kaye.
Bola Tinubu ya taya Adeleke murnar lashe zaɓen Osun, ya bukace shi da haɗa kan jama’a, yayin da ya yaba wa INEC da jami’an tsaro kan zaɓe mai inganci.
Mawaki Davido ya gargadi Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, bayan nasarar Adeleke a Osun, yana mai cewa ya shirya domin mayar masa da martani kan kalamansa.
James Faleke ya musanta zargin Davido na cewa ya matsa wa hukumar INEC lamba kan sakamakon zaben Osun, inda ya ce ya je jihar ne domin tallafa wa APC.
Jihar Osun
Samu kari