Sarkin Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kudirin dokar kirkiro zababbin kananan masarautu 3 a jihar bayan majalisar dokoki ta amince da shi.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Laraba domin fara sauraron kararrakin da ke gabanta kan rikicin masarautar Kano.
Gwamnatin Kano ta ce ba ta yi mamakin hukuncin kotu da ya tabbatar da nadin Sarki Muhammadu Sanusi II ba, inda hadimin gwamna Abba ya ce an yi daidai.
Majalisar jihar Kano ta gabatar da kudirin samar da sarakuna guda uku masu girman daraja ta biyu da za su ƙasa ƙarƙashin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya bayyana kuskuren da aka yi tun farko kan mayar da Sanusi II sarauta inda ya ce shi ba ɗan sarki ba ne domin gadonta ake yi.
Bayan yanke hukunci kan dambarwar sarauta, Kungiyar Kano Democratic Vanguard ta ce hukuncin abin kunya ne ga bangaren shari'a ganin yadda aka nuna son kai a fili.
Babbar kotun jihar Kano ta umarci sarakuna 5 da aka tsige a Kano su mayar da kayan sarautar da ke hannunsu ga Gwamnatin jihar ko Sarki na 16 Muhammadu Sanusi.
Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta kawo karshen rikicin masarautar Kano, ta yanke hukunci a yau Litinin na haramtawa Sarki Ado Bayero bayyana kansa da sarki.
Gamayyar kungiyoyin matasan Kano (KYC) ta yi ikirarin cewa gobarar da ta tashi a fadar Sarkin Kano Sanusi II ya nuna cewa ubangiji bai ji dadin dawo da shi ba.
Sarkin Kano
Samu kari