Majalisar dattawan Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa Sanata Abdul Ahmed Ningi na Borno ta Tsakiya ya ce babu dalilin da zai sa kudin masu aikin kwangila na gwamnati za su ki fito wa.
Majalisar Dattawa za ta duba ƙudurori 31 kan kirkirar sabbin jihohi, 'yan sandan jihohi, da 'yancin kananan hukumomi a zaman jin ra'ayoyin jama'a na watan Yuli.
Kotun tarayya ta bai wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan belin N50m. Ana tuhumar 'yar majalisar da ƙaryar cewa Akpabio da Yahaya Bello na kitsa kashe ta.
Kungiyar sanatocin Arewa (NSF) ta yi Allah wadai kan hare-haren da 'yan bindiga suka kai a Benue. Kungiyar ta bukaci gwamnati ta ba sojojin kayan aiki na zamani.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun sake kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Ihima a Kogi inda yan sanda sun cafke mutum ɗaya.
A labarin nan, za a ji cewa Majalisar kasar nan ta ce ta gama aikin da ya dace a kan kudurorin haraji, kuma tuni aka aika su teburin shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya domin yaki da matsalar tsaro. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta soki matakin.
Za a ji majalisar dokoki za ta duba yiwuwar samar da tsaro a Najeriya ta hanyar duba wasu daga cikin dokokin ƙasa, daga ciki har da batun yan sandan jihohi.
Ana ta yada jita-jitar cewa ba a rera taken Najeriya ba a ranar dimukraɗiyya da Bola Tinubu ya ziyarci gamayyar majalisa domin yin jawabi na musamman.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari