NLC
Yayin da kungiyar kwadago ta shiga yajin aikin gama gari a wannan Litinin din, mambobinta sun tilastawa makaranta da bakuna bin umarnin yajin aiki a Kaduna.
An wayi gari babu jirgin ƙasan da ya shiga ko ya fita daga Abuja yayin da ma'aikata suka ƙauracewa wuraren ayyukansu saboda yajin aikin da ƴan kwadago suka fara.
Rahotanni sun bayyana an kwashi 'yan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas bayan da kungiyar kwadago ta NLC ta dura bankin tare da fatattakar jama'a.
Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta umarci mambobinta da su shiga cikin yajin aikin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara a fadin kasar nan.
Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), reshen kungiyar NLC, sun katse ruwa da wuta na ginin a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara.
Kungiyar kwadago sun sun kulle asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke jihar Kano sakamakon yajin aiki. Marasa lafiya da dama sun koka.
Kungiyar likitoci ta kasa (NMA) reshen Kano ta umarci mambobinta su fito su ga marasa lafiya a asibitocin dake jihar, ta umarci ‘ya’yanta su bijirewa yajin aiki.
Kungiyoyin kwadago na ci gaba da gudanar da yajin aiki a fadin Najeriya. Kungiyar ma'aikatan majalisar tarayya ta kulle majalisa a ranar Litinin.
A safiyar yau Litinin ne ma’aikatan hukumar babban birnin tarayya Abuja suka rufe kofar sakatariyar hukumar da ke kan titin Kapital 11, Garki, Abuja.
NLC
Samu kari