Hukumar yan sandan NAjeriya
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi artabu da 'yan banga masu raka manoma kai amfanin gona a jihar Neja. Sun hallaka mutum bakwai daga cikinsu.
Gwamna Otti na jihar Abia ya nuna damuwa kan yadda yan bindiga da masu garkuwa suka addabi al'umma inda ya yi gargadi tare da shirin yin garambawul.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi wa 'yan sandan jihar Kano sha tara ta arziki. Barau ya ba su babura domin inganta ayyukansu.
Wasu fusatattun mutane sun bankawa wasu masu karbar kudaden haraji wuta a ajihar Anambra. Mutanen sun dauki matakin ne bayan an rasa ran wani mutum.
Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta kama ɓarawon da ya ke cakawa yan acaba makami a kayi ya kwace musu babur. Ya sace babur kirar Bajaj.
Wasu 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan wani matashin lauya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun bi matashin lauyan har gida sannan suka bude masa wuta.
Kotun majistare da ke Ibadan a jihar Oyo ta tsare wasu mutane hudu kan neman bata sunan sarkin Ogbomoso da suke zargin yana neman haddasa fadan addini.
An samu kuskuren rashin fahimta tsakanin jami'an tsaro na 'yan sanda da 'yan banga a jihar Anambra. Jami'an tsaron sun bude wuta ga junansu a cikin dare.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kashe mutum guda yayin da faɗa ya kaure tsakanin wasu jami'anta da ke bakin aiki da wani sojan Najeriya a jihar Ebonyi.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari