Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wata Farfesar Jami'ar Maiduguri mai suna Ruth Wazis bayan ta gamu da tsautsayi a cikin garejin mota.
Kimanin matafiya 20 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya a kan hanyar Sagamu-Ijebu-Ode a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na dare.
An kubutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Lahadi bayan wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Guto da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Dan sanda, Ibrahim Ezekiel Sini ya samu kyauar makeken fili a Abuja bayan ya ki karbar cin hanci domin samun aminci a cikin zuciyarsa da kare mutuncin kansa.
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon tayar da bama-bamai a jihar Borno ya karu. Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta ce an rasa rayukan mutum 18.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wata 'yar kunan bakin wake ta tayar da bam yayin da ake zaman makoki a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a Arewa maso Gabas.
Wasu makiyaya dauke da makamai sun kai farmaki kan wasu kauyukan jihar Jigawa a Arewacin Najeriya. Makiyayan sun raunata mutum takwas tare da lalata gonaki.
'Yan bindigaar da ake wa taken ba a san ko waye ba sun sake kai hari shingen binciken ababen hawa a birnin Aba, jihar Abia, sun hallaka ƴan sanda biyu.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar kama mutum buyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari