Hukumar yan sandan NAjeriya
Gwamnatin jihar Osun ta sanar da cewa an yi kutse a lambar wayar Gwamna Ademola Adeleke inda ta gargadi jama'a su yi hankali da duk wani taimako da za a bukata.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta dauka mataki kan duk wanda ya fito tattakin ranar Ashura a jihar. Ta ce hakan na kawo tashin hankali.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare kan bayin Allah a jihar Anambra. 'Yan bindigan sun hallaka mutum daya tare da sace wasu mutum hudu.
Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta yi ram da wasu iyayen da su ka sa dansu a kasuwa domin su samu kudin ficewa daga kasar nan saboda matsin rayuwa.
Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da cafke barawon babur da ya sace abin hawa a asibiti. Bayan tsananta bincike an same shi da sauran baburan sata shida.
Shugaban jami'ar Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Armaya'u Bichi ya zargi wasu ma'aikatan jami'ar da aiki da 'yan ta'adda ta hanyar ba su bayanai.
Jami'an ƴan sanda sun yi ram da wani dagaci a yankin karamar hukumar Nangere a jihar Yobe bisa zargin yasa an kashe direban motar tarakta a gona.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke matashin da take zargin ya kashe tsohuwa mai shekaru 60. An kashe Safiya Yunusa ne a cikin gidanta da makami a Toro.
'Yan ta'adda dauke da bindigu sun yi shigar mata inda suka sace mutane masu yawa a jihar Katsina. 'Yan ta'addan sanye da hijabai sun kai harin ne a Safana.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari