Jihar Niger
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa bayan mutuwar mutane a iftila'in hatsarin jirgin ruwa dauke da masu bikin Maulidi a jihar Niger.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Neja, ya umarci a gano dalilin yawaitar haɗurra a Najeriya.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya nuna takaicinsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar. Ya yiwa iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su ta'aziyya.
Ta cikin wannan labarin, za ku ji cewa masu ninkawa a jihar Neja sun gano karin mutane takwas daga cikin masu zuwa maulidi da kwalekwalensu ya kife a makon nan.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja watau NSEMA ta sanar da cewa zuwa yanzu an ceto mutum 150 daga ruwa bayan kifewar jirgin yan Maulidi a Neja.
Yan Maulidi sama d 300 sun samu mummunan hadarin jirgin ruwa a jihar Neja yayin da mutane 150 suka rasu. Mutanen sun samu hadarin ne yayin tafiya Maulidi da dare.
Hasashen yanayi da hukumar NiMet ta fitar a ranar Talata a Abuja ya nuna cewa za a zabga ruwa da tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, da sauransu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Neja (NSEMA) ta fitar da rahoton barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar. Akalla mutane 11 sun mutu yayin da aka yi asara mai yawa
Ambaliyar ruwa a karamar hukumar Mokwa a jihar Neja ta cinye kayuka kusan 100, ruwa ya malale makarantu da asibitoci da dama, ruwa ya lalata gonaki da yawa.
Jihar Niger
Samu kari