Jihar Niger
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da fasinjoji ciki har da kwamishina a hukumar zabe.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari gidan Sarkin Fulanin jihar Neja. 'Yan sandan jihar sun kwato wasu mutane da aka sace suna kan tafiya a kan hanya.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya rasa daya daga cikin hadimansa. Gwamnan ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin wanda ya rasu.
NNPC ya samu N318.05bn daga Janairu zuwa Agusta, 2025 don nemo mai a yankunan Sokoto, Neja da wasu hudu, wanda ya zama 30% na ribar PSC daga rabon FAAC.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan bindiga a jihar Neja. Sojojin sun samun nasarar dakile harin na 'yan bindiga tare da kashe da dama daga cikinsu.
Kungiyar matasan Kiristoci ta yi fatali da dokar haramta wa'azi a jihar Niger tana cewa kwata-kwata ba ta dace ba, tana nuna wariya, kuma zalunci ce.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar kula da jarrabawa ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar da dalibai su ka rubuta a ranar Laraba, 17 ga watan Satumba, 2025.
Hukumar NiMet, ta fitar da hasashen ruwan sama da zai sauka a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025, inda ta ce jihohi 13 na Arewa za su samu ruwan daga safe zuwa dare.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ce 'yan Arewa za su bada wa 'yan siyasa irinsu Nasir El-Rufa'i da Aminu Waziri Tambuwal kasa a ido kan zaben Tinubu.
Jihar Niger
Samu kari