Nasir Ahmad El-Rufai
Peter Obi ya mika bukatar yin takara wa'adi daya ga gamayyar 'yan adawa a Najeriya. Obi ya ce zai yi takara sau daya ba tare da yin tazarce ba a 2031.
An hana su Atiku dakin taron kaddamar da ADC a Abuja ba zato ba tsammani. 'Yan adawar sun ce ba za su ja da baya ba yayin da suka zargi sa hannun gwamnati.
Ƙungiyar adawa ta Atiku ta zaɓi ADC don doke Tinubu a 2027, tare da naɗa David Mark da wasu ƙwararru a matsayin shugabanni, yayin da take kuma neman rajistar ADA.
Wasu 'yan jam'iyyar ADC a Najeriya sun yi watsi da maganar hadakar 'yan adawa da aka kulla. Sun ce ba a tuntube su ba kafin a yi maganar hadaka don kifar da Tinubu.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya ce za su mayar da hankali kan samar ilimi mai inganci da adalci a Najeriya yayin da ya yi jawabin fara aiki a Abuja.
A wannan labarin, za a ji cewa APC reshen jihar Sakkwato ta bayyana cewa ba ta fargabar hadakar da 'yan adawa ke kokarin hadawa gabanin zaben 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kalamai masu zafi kan minisotcin da Shugaba Bola Tinubu ya nada a gwamnatinsa. Ya ce ba su da inganci.
A labarin nan, za a ji cewa jagora a APC, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa babu wanda zai iya shaida wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu gaskiya.
Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Alhaji Shehu Gabam, ya yi fatali da batun dakatarwar da aka yi masa daga kan mukaminsa. Ya ce har yanzu shi ne shugaba.
Nasir Ahmad El-Rufai
Samu kari