Nadin Sarauta
Cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan wasa da iko da kuma darajar da Sultan ke da shi musamman a idon Musulman Najeriya.
Mai shari’a K.B. Olawoyin na babbar kotun Oyo ya haramtawa Sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi Olaoye tsige babban limamin Ogbomoso, Sheik Teliat Yunus Ayilara.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa hakiman da suka shigar da kara bayan tsige su sun makara. Kwamishinan shari'a na jihar ne, Barista Nasiru Binji ya fadi haka.
Shugaban kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bukaci a soke dokar da ta ba gwamnatin jihar Sokoto damar sauke Sarkin Musulmi daga kujera.
Rikici ya barke tsakanin masu nadin sarki a yankin Ofe da ke karamar hukumar Ose a Ondo inda suka koka kan yadda ake kokarin ƙaƙaba musu wani a matsayin sarki.
Yayin da rikicin masarauta ke kara kamari a Sokoto, babbar kotun jiha ta dakatar da gwamna Ahmed Aliyu daga tsige hakimai biyu da ta dakatar a baya.
Kudurin sabunta dokar Masarautar Sokoto ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren majalisar Sokoto. Ana fargabar kudurinzai rage ikon Sarkin Musulmi
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya nemi a sanya masarautu a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya domin kare su daga barazanar rugujewa.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai kalubalanci Gwamnan Kano Ganduje a 2020 lokacin da aka tsige shi ba saboda rayuwarsa za ta iya kuntata.
Nadin Sarauta
Samu kari