Nadin Sarauta
Majalisar sarakunan gargajiya na Kudancin Najeriya ta yi Allah wadai kan kisan gillar da miyagun 'yan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.
An yi ta yada hotunan yadda aka fara sabunta fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da ke Nassarawa duk da rigimar masarauta da ake ciki a jihar.
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya amince da nadin Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi bayan rasuwar mahaifinsa.
Mun tattaro bayanan manyan sarakunan Najeriya 7 da suka rigamu gidan gaskiya a cikin watanni 8 na shekarar 2024 da muke ciki. Mutuwar Sarkin Gobir ta girgiza jama'a.
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya yi karin girma ga wasu sarakuna har guda shida da ke karkashinsa zuwa matsayi daban-daban a jihar.
Masarautar Zazzau ta fitar da sanarwar rasuwar Hajiya Habiba, uwar gidan marigayi sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris. An fara shirye-shiryen jana'izarta.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya samu sarautar Sardaunan Ilorin. Mai martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari ya ba gwamnan wannan sarauta.
Kwanaki hudu kacal da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya, masu nadin sarauta a masarautar sun rubuta wasiku ga masu sha'awar neman kujerar marigayin.
Sarki Muhammadu Sanusi ya kai ziyarar ta'aziyya fadar marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya inda ya ce tabbas ba zai manta da Mai Martaba ba.
Nadin Sarauta
Samu kari