Kwanaki da Rasuwar Mahaifiyarsa, Yaron Sarkin Zazzau, Dan Isa, Ya Kwanta Dama
- Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karbi rayuwar Dan Isan Zazzau, Umar Shehu Idris a ranar Talata, 8 ga watan Oktobar 2024
- Masarautar Zazzau ta sanar da cewa marigayi Alhaji Umar ya rasu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Kaduna-Abuja
- Marigayi Dan Isan Zazzau ya rasu yana da shekaru 41 a duniya kuma da ne ga marigayi sarkin Zazzau na 18, Mai martaba Shehu Idris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - An shiga cikin tsananin alhini a garin Zazzau da kewaye yayin da aka samu labarin rasuwar Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris.
Masarautar Zazzau ta sanar da cewa Allah ya karbi rayuwar Alhaji Umar wanda da ne ga marigayi Sarki Shehu Idris a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba.
Dan Isan Zazzau ya rasu
A cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar a shafinta na X ta bayyana cewa Dan Isan Zazzau ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na masarautar Zazzau, Mallam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar ta ce hatsarin ya afku ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Mallam Kwarbai ya ce:
"Cikin alhini da mika wuya ga hukuncin Allah, Masarautar Zazzau na sanar da rasuwar Alhaji Umar Shehu Idris, Dan Isan Zazzau.
"Ya rasu ne da yammacin yau (Talata) a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan titin Kaduna zuwa Abuja."
'Dan Isa: Masarautar Zazzau ta magantu
Kafin rasuwar Alhaji Umar Shehu Idris, shi ne mataimakin sakataren majalisar masarautar Zazzau, a cewar sanarwar.
Wani rahoto da jaridar Aminiya ta fitar ya nuna cewa Dan Isan Zazzau ya rasu ne yana da shekaru 41 a duniya kuma ya bar mata biyu da 'ya'ya biyu.
Sanarwar ta ce nan gaba kadan za a sanar da lokacin da za a yi sallar jana'izar marigayi Dan Isan Zazzau.
Matar marigayi sarkin Zazzau ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar Hajiya Habiba, uwar gidan marigayi sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris rasuwa ranar Juma'a, 30 ga watan Agustan 2024.
Bayanai sun ce daga cikin 'ya'yan marigayiya Hajiya Habiba Shehu da matar sarkin Zazzau na yanzu, Ahmed Nuhu Bamalli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng