Nadin Sarauta
Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta mamaye gidan Galadiman Kano da ke Galadanci a karamar hukumar Gwale, bayan naɗin muƙamin har biyu a jihar.
An nada Munir Sanusi Bayero da Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano yayin da jami'an tsaro ke sintiri a harabar gidan sarauta a Galadanci.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alh. Bashir Yusuf Madaki a matsayin Sabon Dagacin Garin Kenfawa.
Sarakunan gargajiya da dama sun fuskanci dakatarwa daga gwamnonin jihohinsu tun watan Janairu 2025 zuwa yanzu saboda zarge-zarge na cin hanci da rashin adalci.
Oluwo na Iwo, Abdulrasheed Akanbi, ya ce Allah kadai ne garkuwarsa, kuma babu wanda zai iya tsige shi ko kashe shi tun bayan hawansa mulki a 2016.
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya dakatar da Sarkin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru, ba tare da bata lokaci ba bisa zargin cin hanci da gazawar shugabanci.
Yayin da Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Babban Daki, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya halarci taron sarakunan Arewa da aka gudanar a birnin Kaduna.
Sarki Taofeek Owolabi na masarautar Obafemi ya gurfana gaban kotu bisa zargin kwacen fili, karɓar ₦75m ba bisa ka'ida ba, sannan ya kuma ƙi amsa gayyatar gwamnati.
Yayin da ake dakon hukuncin kotu kan rigimar masarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa kafa hukumar raya kiwo da makiyaya ta kasa.
Nadin Sarauta
Samu kari