Masu Garkuwa Da Mutane
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta dakile hare-hare biyu da aka kai a Sabuwa, inda ta ceto mutum 28. Amma 'yan ta'adda sun kashe mutane uku a harin.
'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago bayan sace su a jihar Zamfara. An sace mutanen ne a karamar hukumar Kaura Namoda.
Gwamnatin jihar Kwara ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane a jihohin Kwara da Kogi. Yan sanda sun ce jami'insu daya ya jikkata.
A Alkaleri, mahaifar gwamnan Bauchi, 'yan bindiga sun kashe mutum ɗaya yayin da suka yi garkuwa da mutane 26. An fara tura masu Naira miliyan 1.5 na kudin fansa.
An sace kansilan APC na Daudawa, Buhari Aliyu a hanyar Funtua, inda ake zargin wani mai baiwa ’yan bindiga bayani ne ya taimaka wajen yin garkuwa da shi.
Rundunar 'yan sandan Kano ta ƙaddamar da 'Operation Kukan Kura', ta kama mutane 98 da ake zargi, tare da kwato kayan sata da miyagun ƙwayoyi, inji CP Bakori.
Jihar Oyo za ta kashe N7.7bn don siyan jiragen yaki guda biyu da za su taimaka wa Amotekun da jami'an tsaro wajen yaki da masu garkuwa da mutane.
Masu garkuwa da mutane sun kashe wani soja yayin da suka je sace ɗan kasar Sin a Kogi. An ce jami'an tsaro sun bi sahun 'yan bindigar bayan wannan farmaki.
'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane uku kuma sun ceto mutane 29 a Kogi, Legas, da Katsina, a wani samame na musamman kan yaƙi da miyagun laifuffuka.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari