Manyan Labarai A Yau
An tabbatar da dan fitaccen attajirin nan, Dahiru Mangal a matsayin dan takarar kujerar Majalisar Katsina ta Tsakiya a Majalisar wakilai bayan kai ruwa rana.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makamai daga hannun tsagerun.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana kuri'un da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai samu a zaben 2027. Ya ce bai da adawa a jihar Kaduna.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da $2.99bn domin gudanar da ayyukan layin dogo a jihohi guda uku.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dawo da shugabannin ADC karkashin jagorancin David Mark a shafinta na yanar gizo bayan hukuncin Kotun Koli.
Wani masani ya ce tsohon tarihin masarautar Kano ne dalilin da ya kawo jinkiri a shari'sr da ake tsakanin bangaren Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi kalamai masu kaushi kan shugaban gwamnatin Jamus. Donald Trump ya caccake shi, kan sukar yaki da Iran.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a sassa daban-daban na Najeriya. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda sama da 200.
Kungiyar Hezbollah ta kai hare-hare kan sojojin Israila a Kudancin Lebanon. Hare-haren na Hezbollah sun yi sanadiyyar hallaka wani soja tare da raunata wasu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari