Manyan Labarai A Yau
NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai ƙarfi da iska a jihohin Arewa da Kudancin Najeriya a yau 4 ga Mayu, 2026, tare da gargaɗi kan ambaliya da haɗarin walƙiya.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta tsayar da dan takararta na Gwamna. APC ta zabi Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na gwamna a zaben 2027.
Jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta samu karuwar manyan 'yan siyasa. Manyan kusoshi a jam'iyyun APC, PRP da NNPP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai ziyarci kasar Amurka. Atiku Abubakar zai je Amurka ne domin tattauna matsalolin da suka addabi Najeriya.
An nemi wasu jami'an sojojin Amurka guda biyu an rasa. Sojojin dai sun je kasar Morocco ne domin gudanar da wani atisaye. Tuni aka fara aikin nemansu.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fitar da jadawalin lokacin gudanar da zaben fidda gwani. Ta bayyana kudaden fom na masu neman takara a inuwarta.
Mai neman takarar kujerar sanatan Kebbi ta Tsakiya karkashin inuwar jam'iyyar APC, Kabiru Sani Giant, ya yi watsi da batun sulhu. Ya ce mutane na son canji.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya yi tsokaci kan batun tattaunawa da 'yan bindiga. Ya bayyana cewa gwamnonin Arewa maso Yamma ba su tattauna da 'yan bindiga ba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan sharuddan da Iran ta mika domin kawo karshen yaki. Trump ya ce Amurka na nazari kan sharuddan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari