Manyan Labarai A Yau
Mai neman takarar gwamnan jihar Gombe karkashin inuwar jam'iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga jam'iyya mai mulki kan zaben 2027.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi magana kan gudanar da zaben fitar da gwani. Ya bayyana cewa a shirye APC ta ke ta gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna.
Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma tsohon Ministan tarayya, Abubakar Malami, ya shiga takarar gwamnan jihar Kebbi a inuwar jam'iyyar ADC.
Jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ta musanta rade radin da ake cewa Jonathan ya bar PDP, domin ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta fara neman Sadiya Umar Farouq, wacce ta rike kujerar ministar jin kai karkashin gwamnatin Marigayi Muhammadu Buhari.
Magoya bayan Malam Nasir Ahmad El Rufai sun fara tara kudi da nufin saya masa fam din takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, sun hada Naira miliyan 45.
Kwamitin tantancewa karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya fara tantance gwamnoni da sauran yan takara a Abuja.
Gwamnatin Turkiyya ta kaddamar da kazamin makami mai dogon zango da zai iya kaiwa zuwa nahiyoyin duniya. Yildirimhan zai iya kai wa mil 3,278 idan aka harba shi.
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Olatunji Disu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin wasu jami'ai biyu da kisan Abubakar Idris Dadiyata.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari