Manyan Labarai A Yau
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Mohammed Bello El-Rufai, ya fito ya yi magana kan ci gaba da tsare mahaifinsa da hukumar ICPC ke ci gaba da yi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin nadi a hukumar NSCDC. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ya sabunta wa'adin Ahmed Audi a shugabancin NSCDC.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa jagoran addini na kasar, Imam Khamenei da manyan jami'an gwamnati na nan a raye.
Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare kan kasar Iran. Hare-haren sun shafi birnin Tehran da wasu birane a Iran. Ayatollah Ali Khamenei ya tsira a hare-haren.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki yan siyasar da ke shiga APC. Ya ce zaben shugaban kasa na 2027 zai kasance tsakanin Tinubu da 'yan Najeriya.
Kasar Israila ta kai hare-hare kan Iran ta sama. Iran ta mayar da martanin cewa za ta kai harin ramuwar gayya mai zafi. Harin na zuwa ne yayin da ake tattaunawa.
Tsofaffin kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf kafin su yi murabus, sun garzaya kotu kan kwace musu motocin da aka yi.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Olawepo-Hashim yayi kira ga Farfesa Joash Amupitan da ya gaggauta yin murabus saboda jadawalin babban zaben 2027.
Rahotanni sun nuna cewa wuta ta kama a wasu sassan fadar Mai Martaba Sarkin Jema'a da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, an fara kokarin kashe wutar
Manyan Labarai A Yau
Samu kari