Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna a jihar Katsina. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makamai.
Fada ya barke tsakanin wasu kungiyoyin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Rikicin ya jawo an hallaka wani jagoran 'yan bindiga tare da mayaka da dama.
Mai neman takarar gwamnan jihar Gombe karkashin inuwar jam'iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga jam'iyya mai mulki kan zaben 2027.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi magana kan gudanar da zaben fitar da gwani. Ya bayyana cewa a shirye APC ta ke ta gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna.
Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma tsohon Ministan tarayya, Abubakar Malami, ya shiga takarar gwamnan jihar Kebbi a inuwar jam'iyyar ADC.
Jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ta musanta rade radin da ake cewa Jonathan ya bar PDP, domin ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta fara neman Sadiya Umar Farouq, wacce ta rike kujerar ministar jin kai karkashin gwamnatin Marigayi Muhammadu Buhari.
Magoya bayan Malam Nasir Ahmad El Rufai sun fara tara kudi da nufin saya masa fam din takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, sun hada Naira miliyan 45.
Kwamitin tantancewa karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya fara tantance gwamnoni da sauran yan takara a Abuja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari