Manyan Labarai A Yau
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi yin tafiya tare da Peter Obi don zaben 2027.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya dauki matakin ladabtarwa kan basaraken da aka samu da laifin aikata damfara inda aka yanke masa hukunci a Amurka.
Bincike ya nuna cewa farashin raguna ya kara tashi a kasuwannin dabbobi a jihar Kaduna yayin da musulmai ke shirye shiryen babbar sallah, mutane sun fara hakura.
Rundunar sojojin Isra'ila ta hukunta wasu sojojinta kan wulakanta mutum mutumin mamar Yesu Almasihu a Lebanon. An tura sojojin zuwa gidan kurkuku.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage shari'ar da ke neman hana tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, neman sake tsayawa takara a 2027.
Fubara Dagogi ya bukaci kotu ta soke babban taron APC na lass biss zargin an taiye masa hakkin tsayawa takarar mataimakin shugaban APC na Kudu maso Kudu.
Dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka jagororin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun samu nasarar ne bayan yi masu ruwan wuta.
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Najeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi karanci ga masu neman shiga jami'a.
Jam'iyyar APC ta zabi tsarin maslaha wajen fitar da yan takara a wasu jihohi. Wannan tsarin ya sa wasu yan majalisu sun rasa tikitin takara, inda suka bar jam'iyyar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari