Manyan Labarai A Yau
'Yan bindiga dauke da makamai sun sake sanya mutanen da ke kauyen Dan Gulbi na karamar hukumar Tureta ta jihar Sokoto. Sun hallaka mutane masu yawa.
Gwamnatin jihar Borno na ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar kwalara a kananan hukumomi daban-daban, fiye da mutum 30 sun kwanta dama.
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da bincike kan takaddamar da ta biyo bayan hotunan bayanan dan takara da hadimin ministan Abuja ya wallafa.
Tsohon babban hafsan hafsoshin sojojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi magana kan 'yan bindigan da ke dora bidiyoyi a yanar gizo.
'Yan bindiga sun yi aika-aika bayan da suka kai wani harin ta'addanci a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka wani basarake a kan hanyar komawa gida.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Jagoran 'yan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon janar a jihar Katsina ya tuntubi iyalansa. Ya bayyana cewa yana so gwamnati ta cika masa wasu bukatu.
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin hadimansa. An bayyana cewa an dakatar da hadiman ne sai baba ta gani.
Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da dakatar da dan majalisar wakilai na mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim kan wasu zarge-zarge.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari