Dakarun Sojoji Sun Yi Nasarar Sheke 'Yan Ta'adda 5 a Jihar Arewa

Dakarun Sojoji Sun Yi Nasarar Sheke 'Yan Ta'adda 5 a Jihar Arewa

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda mutum biyar a yayin wani artabu a jihar Taraba
  • Jajirtattun sojojin sun kuma yi nasarar daƙile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane da mugayen ƴan ta'addan suka yi
  • Bayan samun nasarar hallaka ƴan ta'addan, sojojin sun kuma ƙwato bindigu da alburusai daga hannun tsagerun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda guda biyar a jihar Taraba.

Sojojin sun kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane a coci tare da ƙwato tarin makamai da alburusai a hannun ƴan ta'addan.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 5 a jihar Taraba Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da hakan ne a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 2 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a jihohi 2 na Arewa, sun lalata sansaninsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ya sojoji suka sheƙe ƴan ta'addan?

Rundunar ta ce sojojin sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan shirin ƴan ta'addan na yin garkuwa da wasu mabiya addinin Kirista yayin da suke dawowa daga wata coci a Wukari a kan hanyar Tor-Tse da Takum.

Sanarwar ta ce dakarun sojojin na Bataliya ta 93 da ke a Wukari cikin dabara sun yi kwanton ɓauna kan ƴan ta'addan a ranar Talata, 2 ga watan Afirilun 2024.

A yayin arangamar da suka yi da ƴan ta'addan, sojojin sun yi nasarar sheƙe ƴan ta'adda guda huɗu.

An ƙwato makamai masu yawa

Bayan kammala musayar wutan, sojojin sun ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu, babbar bindiga guda ɗaya da jigida guda biyu ta bindiga ƙirar AK-47.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a ranar 27 ga watan Maris 2024, dakarun sojojin sun yi arangama da ƴan ta'adda a gundumar Chanchanji cikin ƙaramar hukumar Takum ta jihar.

Kara karanta wannan

DHQ: Sojoji sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigar da suka sace ɗaliban Kuriga

Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan inda suka sheƙe mutum ɗaya tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida guda ɗaya da wayar hannu guda ɗaya.

Kwamandan ƴan ta'adda ya miƙa wuya

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan ƴan ta'addan Boko Haram, Mallam Yathbalwe, ya tuba ya mika wuya ga dakarun sojojin Operation Hadin Kai a jihar Borno.

Ƙasurgumin ɗan ta'addan ƙungiyar Boko Haram ɗin ya jima yana aikata ta'addanci kan bayin Allah a yankin Gwoza da garuruwan da ke kewayen Tsaunin Mandara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel