Kaduna: Dakatacciyar Shugabar Matan APC Ta Sake Taso Uba Sani a Gaba

Kaduna: Dakatacciyar Shugabar Matan APC Ta Sake Taso Uba Sani a Gaba

  • Maryam Suleiman, shugabar mata ta jam'iyyar APC a jihar Kaduna, ta tofa albarkacin bakinta kan halin da ta tsinci kanta a ciki
  • A wata hira da ta yi da ita a baya-bayan nan, ta ce ko kaɗan ba ta yi nadama kan sukar da ta yi wa Gwamna Uba Sani ba
  • An dai dakatar da ita ne bayan ta fito fili ta soki gwamnan bayan ya yi iƙirarin cewa Malam Nasir El-Rufai ya bar jihar da ɗimbin bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakatacciyar shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Maryam Suleiman, ta ce ba ta yi nadamar sukar da ya yi wa Gwamna Uba Sani ba.

Kara karanta wannan

Think Tank: Ƴan Arewa ba za su iya hana Bola Tinubu lashe zaben 2027 ba saboda abu 1

A wata hira ta wayar tarho da jaridar The Punch a ranar Litinin 1 ga watan Afrilu, Maryam ta yi magana kan dakatarwar da aka yi mata.

Shugabar matan APC ta magantu kan dakatar da ita
Maryam ta hakikance cewa abin da Uba Sani ya yi cin amana ne Hoto: Nasir El-Rufai, Maryam Suleiman, Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Ta bayyana dakatarwar da jam’iyyar ta yi mata kan sukar gwamnan a matsayin haka Allah ya so, inda ta ƙara da cewa ko kaɗan ba ta damu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa APC ta dakatar da Maryam Suleiman?

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna suka sanar da dakatar da Maryam Suleiman, bayan ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Dakatar da ita ya biyo bayan sukar da ta yi kan iƙirarin da gwamnan jihar Uba Sani ya yi na cewa gwamnatinsa ta gaji bashi mai yawa daga El-Rufai.

Shin Maryam ta damu kan dakatar da ita?

Sai dai a ranar Litinin, shugabar matan ta ce ba ta damu da dakatarwar da aka yi mata ba, tana mai jaddada cewa ta faɗi gaskiya.

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: Shehu Sani ya fadi gaskiyar lamari kan bashin Kaduna

Da take ƙarin haske, ta bayyana cewa a shafukan sada zumunta ta samu labarin dakatar da ita kuma har yanzu ba a sanar da ita a hukumance ba.

Maryam ta ce tana kan bakanta kan abin da ta fada a cikin faifan bidiyon. Tayi nuni da cewa abin da gwamnan ya yi cin amana ne ƙarara.

A kalamanta:

"Ban yi nadama a kan sukar da nake yiwa Gwamna Sani ba. Ina godiya ga Allah kan duk abin da ya faru.
"Na ji an dakatar da ni ne kawai a shafukan sada zumunta. Har yanzu ba a ba ni takardar dakatarwa ba.
"Ko ma dai menene, na tsaya kan abin da na faɗa game da gwamna. Ban yi nadama ba ko kaɗan. Ban damu ba kan abin da na yi saboda na san na faɗi gaskiya."

Yaron El-Rufai ya soki Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bashir Nasir El-Rufai ya yi martani mai zafi kan bashin da Gwamna Uba Sani ya ce El-Rufai ya bari a Kaduna.

Ɗan tsohon gwamnan na Kaduna ya yi nuni da cewa gwamnan bai san inda aka dosa ba inda yake fakewa da bashi domin rufe rashin cancantarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel