Manyan Labarai A Yau
Babban bankin Najeriya (CBN) ya dauko bincike kan basussukan $7bn da tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, ya bari. EFCC na cikin masu bincike.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya koka kan yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane. Ya bayyana su a matsayin 'yan ta'adda wadanda za a kawo karshensu.
Gwamnan jihar Zamfara ya koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita jihar. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bi hanyoyin kawo karshen matsalar.
Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ta yi sabom shugaban riko na kasa. Ahmed Ajuji ya maye gurbin Alhaji Abba Kawu Ali bayan ya yi murabus.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sha alwashin hukunta 'ya'yanta da suka ci dunduniyarta a lokacin babban zaben da aka gudanar a shekarar 2023.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ta sanar da cewa ta samu nasarar ceto wasu mutane da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su. Mutanen an tsare su ne a daji.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai halarci jana'izar sojojin Najeriya da aka kashe a yankin Okuama na jihar Delta. Za a yi jana'izar a birnin tarayya Abuja.
Femisohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu addu'a domin ta samu nasara.
Wasu kwamandojin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mika wuya a hanjun dakarun sojoji a jihar Borno. Sun kuma mika makaman da suke ta'addanci da su.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari