Matashi Ya Salwantar da Ran Yayansa a Bauchi, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- Wani matashi ya biyewa zuciya ya aikata aikin dana sani bayan ya hallaka yayansa a jihar Bauchi
- Lamatin ya auku ne bayan faɗa ya ɓarke a tsakanin na si sakamakon shan Sholo da yayan nasa yake yi a cikin ɗakinsu
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce tuni jami'anta suka cafke matashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Jami'an ƴan sanda a jihar Bauchi sun cafke wani matashi mai suna Isyaku Babale, mai shekara 30 a duniya bisa zargin hallaka yayansa.
Matashin wanda yake zaune a Anguwan Dawaki cikin birnin Bauchi, ya aikata wannan ɗanyen aikin ne bayan sun samu saɓani a tsakaninsu, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
Yadda matashin ya aikata ɗanyen aikin
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris 2024, lokacin da wanda ake zargin ya buƙaci yayan nasa ya daina shan Sholi a ɗakinsu saboda warin ya dame shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya sanya su duka suka harzuƙa inda suka fara ba hammata iska a tsakaninsu.
Jim kaɗan bayan fara faɗansu, sai wanda ake zargin ya ɗauko wani abu mai kaifi da ake zargin wuƙa ce ya ɗabawa yayan nasa a cikinsa.
Bincike ya bayyana cewa sun saba ba hammata iska ta hanyar yin amfani da makamai masu hatsari.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Jaridar Vanguard ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, 1 ga watan Afirilun 2024.
Ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne bayan DPO na ofishin ƴan sandan cikin garin Bauchi, ya samu rahoto kan ɓarnar da ya aikata.
A kalamansa:
"Nan da nan aka tura jami'ai zuwa wajen da lamarin ya auku. Sun kai wanda abin ya shafa zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Ƴan sanda sun yi kamu
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta cafke wasu mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan jami’anta a yankin Ughelli da ke jihar Delta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng