Manyan Labarai A Yau
Majalisar dattawa ta Najeriya za ta gudanar da bincike kan mutuwar da wasu masu hakar ma'adanai suka yi a jihar Neja, bayan dutse ya zaftaro musu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne sun hallaka mutum uku bayan sun tare motarsu a kan hanya a jihar Yobe.
Wasu mutane da ke tserewa harin 'yan bindiga a jihar Neja sun rasa rayukansu a cikin ruwa. Mutanen sun rasu ne bayan kwale-kwalen da suke ciki ya yi hatsari.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyyar za ta rika amfani da rajistar da take da ita wajen ba da mukamai.
An jibge jami'an tsaro yayin da kotu ta fara zamanta domin sauraron karar da ake yi kan rikicin masaurautar Kano. Jami'an tsaro sun hana zirg-zirga.
Tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da 'yan kwadago ta tashi ba tare da an cimma matsaya ba. Za a sake zama domin tattaunawa.
Wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Henry Marah, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai ya karbo kudade ba tare da yin aikin komai ba.
Najeriya ta sauya taken kasarta bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar. Akwai kasashen da suka sauya taken kasarsu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka wani fasto tare da wasu mutum hudu a harin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari